Skip to main content
NGOsource 501(c)(3) Equivalent ACHPR Observer · N°553Observateur CADHP · n° 553 Co-Chair · SEA-T Advisory CouncilCoprésidence · Conseil consultatif SEA-T TransparencyTransparence Candid Platinum Seal 2026Sceau Platinum Candid 2026
RFLD members and partners at a women’s rights meeting
Maputo Protocol · Hausa

Yarjejeniyar Maputo da harshen Hausa

The Maputo Protocol in Hausa · RFLD translation, 2022, web version

Web version of the RFLD translation (2022). This is the text of RFLD’s printed Hausa booklet, put online so that it can be searched, read on a phone and used with screen readers. Only the texts adopted by the African Union are authentic.

Listen in Hausa

Contents
  1. Kudiri na farko: Ma'anoni
  2. Kudiri na 2: Kawar da duk wani nau’i na wariya ga Mata
  3. Kudiri na uku: Incin kare mutunci
  4. Kudiri na 4: Incin rayuwa, kare mutunci da tsaro
  5. Kudri na biyar 5: Kawar da dabi’u masu cutarwa
  6. Kudiri na shida: Aure
  7. Kudiri na bakwai: Rabuwar wurin zama, saki ko soke aure
  8. Kudiri na takwas: Samun adalci da kariya daidai gwargwado a gaban doka
  9. Kudiri na tara 09: Incin shiga harkokin siyasa da na yanke sharwara
  10. Kudiri na 10: Inci na samun Tsaro
  11. Kudiri na 11: Kare mata a cikin yanayi na rikici da makamai
  12. Kudiri na 12: Incin bada ilimi da horo
  13. Kudiri na 13: Inci na tattalin arziki da kariya ta zamantakewa
  14. Kudiri na14: Incin samun kula da lafiya da kuma kula da lafiyar mata
  15. Kudiri na 15: Incin bada kariya a fannin samar da abinci
  16. Kudiri na 16: Incin samun gidan kwana na gari
  17. Kudiri na 17: Incin kasancewa cikin yanayi na kyawawan al‘adu
  18. Kudiri na 18: Incin kasancewa cikin yanayi kyaukyawa
  19. Kudiri 19: Inci na samun ci gaba mai dorewa
  20. Kudiri na 20: Incin matar da mijinta ya rasu
  21. Kudiri na 21: Inci na samun gado
  22. Kudiri na 22: Bada kariya ta musamman ga mata tsofaffi
  23. Kudiri na 23: Bada kariya ga mata nakasassu
  24. Kudiri na 24: Kariya ta musamman ga mata a cikin damuwa
  25. Kudiri na 25: Saka mutane cikin incinsu
  26. Kudiri na 26: Aiwatarwa da bi sau da kafa
  27. Kudiri na 27: Fasarawa
  28. Kudiri na 28: Saka hannu, amincewa da kasancewa mamba
  29. Kudiri na 29: Soma aiki na yarjejeniyar
  30. Kudiri na 30: Gyara da yin bita
  31. Kudiri na 31: Matsayin wannan yarjejeniya
  32. Kudiri na 32: Mataki na wucin gadi

Gabatarwa Kungiyar Mata masu fada a ji mai kula da ci gaba ta (RFLD) tare da haɗin gwiwa EQUALITY NOW wato (Daidaito YAN- ZU), suna aiki don aiwatar da tsarin da aka yi wa suna « GABA DAYANMU MU BADA GOYON BAYA GA YARJE- JENIYAR MAPUTO ». Kuma hukumar raya kasa da kasa ta Sweden (SIDA) ce ta dauki nauyin wannan tsari .

Tsarin nan da aka yi wa suna « Tous pour le Protocole de Maputo wato GABA DAYANMU MU BADA GOYON BAYA GA YARJEJENIYAR MAPUTO » a Nijar zai bayar da gudunmawa ga :

– Bada shawarwari ko isar da koke ga hukumomi don amincewa da yarjejeniyar Maputo.

– Ba da gudummawa wajen ganin an samu ingantaccen sani daga bangarori daban-daban (kaman jama’ar kasa, da sauran gungu-gungu na kungiyoyi) kan ilimin kare lafiyar mata yayin jima'i da kuma haihuwa;

Manufofi na musamman

1. Bada shawarwari ga hukumomi don su gane mahimmancin yarjejeniyar ta yadda za su saukaka aiwatar da ita a nan Nijar;

2. Bai wa mata shugabannin karin ilimi kan abubuwan da ke cikin yarjejeniyar ta Maputo don su kuma su bayar da shawarwari mai inganci ko isar da kokensu ga hukumomi;

3. Wallafa wannan yarjejeniya ta Maputo ta kafofin watsa labarai don kowa ya fahimta da abubuwan da ta kumsa masu mahimmanci ga lafiyar mata da incinsu.

Sakamakon da ake sa ran samu

1. Magabata na siyasa su dauki matakai masu karfi da za su bada damar gaggauta amincewa da yarjejeniyar ta Maputo.

2. Kungiyoyi su rinka aikin fadakarwa da bayar da shawarwari masu inganci domin sanar da wannan tsari na inci da lafiya a fannin jima’i da haihuwa.

3. Mata da yan mata su samu sani kan abun da ya shafi harkokin jima’i da kare lafiyarsu, su iya isar da kokensu ga gabata ta yadda masu izinin daukan matakai su rinka kulawa da abubuwan da suka shafi kula da lafiyar mata a fadin kasa baki daya.

4. Haɓaka ƙididdiga da ingancin labarai kan kyawawan halaye na mata da shawarwari masu amfani ga hukumomin ko gwamnati kan hanyoyin da za a bi don kare haƙƙin mata a matsayin wani abin da zai taimaka wajen haɓaka daidaiton jinsi da ƙarfafa kariyar incin mata a Nijar;

5. Kara adadin bayanai masu inganci (wallafe-wallafe) bisa kyawawan ayyuka na mata da bayar da shawarwarin da suka dace ga ma’aikatu na gwamnati kan batun kare hakkokin mata wanda za su bada damar kula da daidaito a fannin abun da ya shafi mata da maza, da kuma fannin cin gashin kan mata a fannoni daban-daban.

Yarjejeniya ta kundin Afirka mai kula da kare incin dan Adam da na al’umma, wanda ya shafi incin mata a Afirka Matsayin kasashe kan wannan yarjejeniya:

Ta la'akari da cewa kudiri na 66 na Yarjejeniya Tarayyar Afirka game da 'Yancin Dan Adam da al‘umma ya tanadi aiwatar da ka'idoji ko yarjejeniyoyi na musamman idan bukatun hakan sun taso, don cike gibin batutuwan da kundin ya kumasa, wanda taron Shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar Tarayyar Afirka karo na 31 na watan Yunin 1995 da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya aminta da shi ta hanyar wani kuduri da taron ya dauka, da shawarar da hukumar kare hakkin dan Adam da al’umma ta Afrika ta tsara wata kan 'yancin mata a Afirka.

Sannan kuma ta la’akkarin cewa mataki na biyu na Kundin Afirka mai kula da incin Dan Adam da na al’umma ya haramta duk wani nau’i na nuna wariya ta hanyar amfani da launin fata, kabila, bambamcin Jinsi, ko na harshe, Adini akida ta siyasa ko wata akida ta daban, Asali na kasa ko na zamantakewa, arziki, Haihuwa da dai sauransu;

A kari da la’akkari da cewa kudiri na 18 na Yarjejeniya ta Duniya kan 'Yancin Dan Adam da al‘umma ya bukaci dukkan kasashe da su kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata da kuma tabbatar da kare 'yancin mata kamar yadda yake kumshe a cikin dukannin sanarwoyi da yarjejeniyoyin kasa da kasa;

Lura da cewa, kudiri na 60 da 61 na Kundin Tarayyar Afirka kan Hakkokin Dan Adam da al‘umma sun amince da ka'idojin yanki da na kasa da kasa kan incin dan adam da na al’umma da kuma wasu dabi’u na Afirka da suka dace da tsarin kasa da kasa na kiyaye incin dan adam da na al'umma, a matsayin mahimman ka'idodi na aiwatarwa da ma fassarar Kundin na Afirka;

Bisa Tunatar da cewa Dukannin tsarin kasa da kasa kan Incin dan Adam da na al’umma sun aminta da kare hakkokin mata, musamman ma sanarwar Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakin Dan Adam, da Yarjejeniyoyin kasa da kasa kan 'yancin jama'a da siyasa da kuma 'yancin tattalin arziki, zamantakewa da al'adu, da Yarjejeniyar kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata da tsarin da ta kumsa, na Kundin Afirka kan 'yanci da jin dadin yara kanana da dai sauransu.

Yarjejeniyoyin da alkawuran kasa da kasa da suka shafi hakkokin mata a matsayin hakkin dan adam, masu dogaro da juna da ba za a iya raba su ba;

Har ila yau, kuduri mai lamba 1325 na kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya game da rawar da mata za su taka wajen inganta zaman lafiya da tsaro;

LURA da cewa hakkokin mata da muhimmancinsu ga ci gaba an kara jaddada su ne a cikin tsarin ayyuka na Majalisar Dinkin Duniyakan Muhalli da ci gaba (a 1992), 'Yancin Dan Adam (a 1993), Yawan jama'a da ci gaba (a 1994), sannan batun ci gaban da kuma zamantakewa (a 1995);

Kara jaddada ka'idar inganta daidaito tsakanin maza da mata kamar yadda ya tanada a cikin kundin tsarin mulki na Kungiyar Tarayyar Afirka, sabon tsarin kawance don ci gaban Afirka, da sanarwoyi gami da kudurori da kuma mahimman matakai da ke nuni da jajircewar kasashen Afirka na tabbatar da cewa matan Afirka sun shiga cikin tsarin ci gaban Afirka a matsayin abokan hulda daidai da yan uwansu maza;

A cigaba da lura da cewa, dandalin aiwatar da ayyuka na Afirka da sanarwar birnin Dakar ta 1994 da dandalin aiwatar da ayyuka na birnin Beijing da kuma sanarwar nan ta shekarar 1995 da suka yi kira ga daukacin kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da suka yi alkawarin aiwatarwa da daukan kwararan matakai wajen kiyaye hakkokin Dan Adam na Mata don kawar da duk wani nau'i na wariya da cin zarafi da ya shafi jinsi;

Sanin muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen kiyaye martabar Afirka bisa ka'idojin daidaito, zaman lafiya, 'yanci, mutunci, adalci, tamakekkeniya da dimokuradiyya.

Ya kasance cikin kanunmu cewa shawarwari, ko sanarwoyi, da yanke shawara da yarjejeniyoyi da sauran dokoki na yankuna da ke da buri na kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata da inganta daidaito tsakanin maza da mata a fannonin da suka dace;

Cikin nuna damuwa kan cewa duk da amincewar da akasarin kasashe mambobi na Afrika suka yi a kan Kundin Afirka na 'Yancin Dan Adam da al’umma da duk wasu ka'idojin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa, da kuma daukan alkawurra da kasashen suka yi na kawar da duk wani nau'i na nuna wariya da cutarwa ga mata, mace a Afirka na ci gaba da fuskantar wariya kuma ana aikata munanan ayyuka a kanta;

Da imanin cewa duk wata al’ada da ke iya kawo cikas ga ci gaban ko kuma yin tasiri wajen hana bunkasar rayuwar mata da ‘yan mata, to dole ne a yi Allah wadai da su tare da kawar da su;

Jajircewa wajen ci gaba da habaka, da kuma kiyaye hakkin mata don ba su damar cin gajiyar dukkan hakkokinsu na ‘yan Adam;

Sun yarda da abubuwa kaman haka:

Kudiri na farko: Ma'anoni

Cikin wadannan yarjejeniyoyi, ana nufin ma’anar:

a) « Acte constitutif », Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Afirka;;

b) « Charte africaine », Kundin Tarayyar Afirka kan kare kakkokin Dan Adam da al’umma

c) « Commission africaine », Kwamitin Tarayyar Afirka mai kula da kare kakkokin Dan Adam da al’umma

d) « Conférence », Majalisar shugabannin kasashe da gwamnatocin Tarayyar Afirka;

e) « Discrimination à l’égard des femmes », duk wani bambanci, nuna wariya, kuntatawa ko bambance-bambancen da ya shafi jinsi, wanda ke da makasudi ko tasirin tawaya ko hana jin dadin rayuwa ga mata masu aure ko marassa aure, na hakkokin dan adam da sauran ‘yanci a kowane fanni na rayuwa;

f) « États », Kasashen da ke cikin Yarjejeniyar ;

g) « Femmes » yan Adam Mata ko ‘yan mata ;

h) « NEPAD Sabon hadin kai don ci gaban Afirka, wanda babban taron ya kirkira;

« Pratiques néfastes », duk wata dabi’a, ko halaye da ke yin illa ga muhimman hakkokin mata, kamar ‘yancin rayuwa, incin samun kula da lafiya, incin samun ilimi, da kare mutunci da ma kariyar gangan jikinta;

« UA », Kungiyar Tarayyar Afirka ;

« Violence à l’égard des femmes », duk wani abu da aka aikata akan mata da ka iya haifar da lahani ko cikas ga mata, Kaman cin zarafi ta hanyar Fyade, tunani ko tattalin arziki ko wata barazanar aikata irin waɗannan ayyukan, ko sanya takunkumi ko kuma tauye ‘yancin na ba gaira ba dalili, walau a cikin rayuwa ta sirri ko a cikin rayuwa ta bainar jama'a, ko a lokacin zaman lafiya, ko kuma a yanayi na rikici ko yaki.

Kudiri na 2: Kawar da duk wani nau’i na wariya ga Mata

Kasashe za su yi yaki da nuna wariya ga mata ta kowane hali, ta hanyar kaddamar da matakan da suka dace a fanni na doka, fannin manyan hukumomi da sauransu. Ta sabili da haka, sun dauki alkawurra kaman haka:

a) Rubuta ka'idar saka daidaito tsakanin maza da mata a fannoni daban-daban, cikin Kundin Tsarin Mulki da sauran fannoni na doka, idan har ba su riga sun yi hakan ba, da kuma tabbacin ana aikatawa;

b) Amincewa da kuma aiwatar da matakan da suka dace na doka, gami da haramtawa da watsi da duk wani nau'i na wariya da ayyuka masu cutarwa da ke gurgunta lafiya da walwalar mata;

(c) Saka abubuwan da suka shafi matsalolin mata na yau da kullun a fannin daukan mataki na siyasa, da na dokoki, tsare-tsarensu ga ayyukan ci gaba da sauran fannonin rayuwa;

(c) daukar matakan gyara, a fannonin da ake ganin akwai wanzuwar nau’in nuna wariya ga mata;

e) Nuna goyon baya ga fusa’o’i na karkara, na kasa, na yanki da ma na nahiya da nufin kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata.

2. Kasashe sun dauki alkawura na sauya salon na dabi’un zamantakewada al'adun mata da na maza ta hanyar ilimantar da jama'a ta hanyar dubarun bada labari, da nufin cimma nasarar kawar da duk wasu halaye masu cutarwa na al'adu da na gargajiya marassa amfani da duk wasu halaye na nuna kaskanci ko nuna fifikon jinsi na wannan ko wancan bangare, kan matsayin mata da maza.

Kudiri na uku: Incin kare mutunci

1. Incin ko wace mace ne, a mutuntata tare da kare hakkokinta cikin tsari na doka.

2. Ko wace mace na da incin a mutuntata a matsayinta na ‘yar Adam da kuma incin bunkasar mutuncinta.

3. Kasashe sun aminta za su kuma aiwatar da matakan da suka dace don hana duk wani cin zarafin mata ko wani wulakanci da ake yi musu.

4. Kasashe sun aminta tare da aiwatar da matakan da suka dace don tabbatar da kare hakkin mata da kiyaye mutuncinsu da kuma kare su daga duk wani nau'i na tashin hankali, musamman cin zarafi ta hanyar saduwa da su ko yi musu fyade.

Kudiri na 4: Incin rayuwa, kare mutunci da tsaro

1. Ko wace mace hakkin ta ne a mutunta rayuwarta, ga tsaron mutuncinta, da mutuncin jikinta.

Dole ne a haramta duk wani nau'i na cin zarafi, azabtarwa, cin mutunci ko wulakanci.

2. Kasahse sun yi alkawarin daukar matakan da suka dace kuma masu inganci domin:

3. Amincewa da ƙarfafa dokokin da suka haramta duk wani nau'i na cin zarafin mata, ko ta hanyar fyade ma’ana yin jima'i ta hanyar tilastawa,

4. aiwatar da duk wasu matakai na doka, gudanarwa, zamantakewa, tattalin arziki da sauran su da nufin kawar da duk wani nau'i na cin zarafin mata;

5. gano musabbabi da sakamakon cin zarafin mata tare da daukan matakan da suka dace don hana su da kawar da su;

6. bunkasa harkokin ilimi da zaman lafiya ta hanyar tsari na koyarwa da sadarwar ta zamantakewa don kawar da abubuwan da ke kunshe a cikin dabi’u na al’adun gargajiya da ake yi na yau da kullum da ka iya sanya rufe idanu kan cin zarafin mata;

7. hukunta masu cin zarafin mata tare da aiwatar da shirye-shirye domin farfado da kariyar hakkokin mata;

8. daukan matakai don tabbatar biyan diyya ga matan da aka zalunta;

9. hanawa da kuma yin tir da Allah wadai da duk nau’i na fataucin mata, tare da hukunta masu aikata wannan aika-aika tare da bai wa matan da suka fi fuskantar wannan matsala kariya.

10. haramta duk wani gwaji na likita ko na kimiyya akan mata ba tare da saninsu ba;

11. ware isassun kudi cikin kasafin kuɗi na kasa da sauransu don bi sau da kafa da nufin hanawa da kawar da cin zarafin mata;

12. a tabbatar cewa, a kasashen da har yanzu ake aiwatar da hukuncin kisa, ba a zartar da hukuncin kisa a kan mata masu juna biyu ko masu shayarwa ba;

13. A tabbatar cewa mata da maza suna da dama ta bai daya yayin tantancesu a matsayin yan gudun hijira sannan suna samun cikakkiyar kariya da fa'idodin da aka aminta da su a karkashin dokar 'yan gudun hijira ta kasa da kasa.

Kudri na biyar 5: Kawar da dabi’u masu cutarwa

Kasashe suna haramtawa tare da yin Allah wadai da duk wani nau'i na ayyuka masu cutarwa da ke yin mummunan tasiri ga 'yancin dan adam na mata kuma wadanda suka saba wa ka'idodin kasa da kasa. Kasashe za su ɗauki duk matakan doka da sauran matakan kawar da wadannan ayyuka musamman:

a) wayar da kan al'umma ta hanyar sadarwa da tsarin bayar da labarai, da ilimimantarwa kan ayyuka masu cutarwa

b) haramtawa ta hanyar matakan doka tare da hukunci, ga masu aikata kaciyar mata, da duk wasu ayyuka masu cutarwa;

c) bayar da tallafin da ya dace ga wadanda abin ya shafa ta hanyar ba su ayyuka na yau da kullun, kamar ayyukan kiwon lafiya, taimako ta hanyar shari'a, shawarwari, isassar kulawa da horars da kwararru don ba su damar daukar nauyi;

d) bada kariya ga matan da ke cikin hadarin fuskantar muyagun dabi’u masu cutarwa da duk wasu nau’i na muzguna wa da cin zarafi.

Kudiri na shida: Aure

Kasashe suna tabbatar da cewa maza da mata suna cin moriyar hakkoki daidai gwargwado kuma ana daukarsu daidai gwargwado cikin auratayya.

Dangane da haka, kasashe za su ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa:

a) ba a daura duk wani auren da bas hi da amincewar dukannin bangarorin da za a daura wa auren ba;

b) Karanci shekaru na auras da diya mace su ne shekaru 18

c) ana kwadaitar da auren mace daya a matsayin mafi kyawun tsarin aure, idan har mutun ya san ba zai iya adalci ba. Ana karewa da kiyaye hakkin mata da ke a cikin aure ciki har da ma'auratan aure fiye da daya;

d) Duk aure kafin a aminta da shi a hukumance, sai an yi mishi takardar aure dai dai da yadda dokokin kasa suka tanadar ;

e) ma'aurata biyu suna zaba ne bisa yarjejeniya tsarin aurensu da kuma wurin da za su zauna;

f) Macen da aka aura tana da incin ta kiyaye sunanta, ta yi amfani da shi yadda ta ga dama, dabam ko kuma ta hada shi da na mijinta;

g) Macen da aka aure tana da inci ta ci gaba da rike takardunta na kasarta ta haihuwa ko kuma ta mallaki na kasar mijinta.

h) Mata suna da inci iri daya da maza dangane da kasar 'ya'yansu, sai dai idan kasashen nasu tsarin ya sha bambam da kuma bukatun tsaron kasa;

i) mace da namiji za su bada gudummawa tare don kiyaye muradun iyali, da tarbiyyar ’ya’yansu;

j)A tsawon lokacin daurin aurensu, mace tana da incin mallakar dukiyarta, ta gudanar da ita yadda take bukata.

Kudiri na bakwai: Rabuwar wurin zama, saki ko soke aure

Kasashe sun yi niyyar aiwatar da tanadin dokokin da suka dace domin maza da mata su more hakkoki iri daya a cikin yanayin rabuwa, saki da kuma raba aure. A wannan yanayin, suna tabbatar da cewa:

a) Rabuwar aure, saki ko soke aure, ana bayyana su ne ta hanyar shari’a;

b) a) namiji da mace suna da inci iri naya na neman raba zaman aurensu, saki ko soke aure;

c) idan aka yi saki, ko warware aure ko kuma rabuwa ta shari’a, mace da namiji suna da hakkpki na ma’amala da ‘ya’yansu. A kowane hali, babban abin da ake son kula da shi, shi ne kiyaye bukatun yaran;

d) idan aka samu rabuwar aure, saki ko warwarewar aure, mace da namiji suna da incin raba dukiyarsu da suka samu tare a lokacin aure daidai gwargwado.

Kudiri na takwas: Samun adalci da kariya daidai gwargwado a gaban doka

Mata da maza suna da inci daidai a gaban doka, kuma suna da 'yancin samun daidaitaccen kariya da fa'idar doka. Kasashe za su dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da:

a) samun ingantacciyar dama ga mata don samun taimako da ayyuka na shari'a da mashara’anta;

b) goyon bayan fusa’o’i na karkara, na kasa, yanki da nahiya da nufin samarwa mata damar samun taimako a ma‘aikatu na shari'a;

c) samar da isassun wuraran bayar da ilimi, tare da bada kulawa ta musamman ga mata da wayar da kan dukkan sassan al’umma kan kiyaye hakkin mata;

d) horas da hukumomi don tabbatar da doka a kowane mataki kan batun aiwatar da daidaito na doka tsakanin maza da mata ;

e) Samun daidaiton wakilcin mata a cibiyoyin shari’a da na tabbatar da doka;

f) sake fasalin dokoki kan ayyuka na nuna wariya don kare hakkin mata.

Kudiri na tara 09: Incin shiga harkokin siyasa da na yanke sharwara

Kasashe za su dauki kyawawan matakai don inganta tsarin tafiyar da harkokin shugabanci ta yadda kowa zai kawo tashi gudunmowa da kuma kasancewar mata daidai gwargwado a harkokin siyasar kasashensu, ta hanyar tabbatar da matakai da tsarin dokokin kasashen suka tanada da sauran matakan tabbatar da cewa:

1- Mata za su shiga cikin dukannin zabukan kasa ba tare da wata wariya ba;

2- A samu wakilci na mata daidai da na maza a dukannin mataki cikin tafiyar da harkokin zabe ;

3- Mata za su kasance abokan hulda daidai wadaida tare da maza a kowane mataki na tsarawa da aiwatar da manufofi na ci gaban kasa.

4- Kasashe su tabbatar da kasancewa mai ma'ana da ingantaccen wakilci da shigar mata a kowane mataki na yanke shawara.

Kudiri na 10: Inci na samun Tsaro

Mata su na da 'yancin samun zaman lafiya, kuma suna da 'yancin shiga cikin tsarin tabbatar da zaman lafiya.

Kasashe za su dauki dukkanin matakan da suka dace don tabbatar da shigar mata masu yawa :

1 a tsarin bayar da ilimi, zaman lafiya da tsarin al’adu na samar da zaman lafiya ;

2 hanyoyi da matakai don rigakafi, da warware rikice-rikice a mataki na karkara, na kasa, yanki, nahiyoyi da ma na kasa da kasa;

3 hanyoyin yanke shawara na karkara, na kasa, na yanki, zuwa nahiyoyi da na duniya don tabbatar da kariya ta gangan jiki, da tunani, zamantakewa da doka na masu neman mafaka, 'yan gudun hijira, da suka dawo da kuma mutanen da suka yi gudun hijira, musamman mata;

4 a duk matakan hanyoyin sarrafa sansanin da sauran wuraren mafaka ga masu neman mafaka, ko 'yan gudun hijira, ko wadanda aka kwaso, ko wadanda suka bar matsugunnansu musamman mata;

5 a duk fannoni na tsarawa, da kuma aiwatar da shirye-shiryen sake ginawa da gyara na bayan rikici.

6 Kasashe za su dauki matakan da suka dace don rage kashe kudi masu yawa a fannin sojoji don karkata su ga ayyukan da al‘ummar kasa za ta amfana, da kuma musamman ma bunkasar rayuwar mata.

Kudiri na 11: Kare mata a cikin yanayi na rikici da makamai

1 Kasashe mambobi sun dauki nauyin mutuntawa, da sa wa a mutunta kai’doji na dokokin jin kai na kasa da kasa da ke aiki a cikin yanayi na rikice-rikice da makamai da ke shafar yawan jama'a, musamman mata.

2 Dole ne kasashe, dangane da nauyin da ya rataya a kansu kuma bisa dokokin jin kai na kasa da kasa, su bada kariya ga fararen hula a cikin yanayi na yaki, ciki har da mata, kuma koma cikin wane rukunin jama’a suke;

3 Kasashe sun yi alkawarin kare matan da ke neman mafaka, 'yan gudun hijira, da wadanda aka kwaso daga wasu wurare ko wadanda suka bar matsugunnansu daga kowane irin nau'i na cin zarafi, fyade da sauran nau'o'i na lalata da matan sannan da tabbatar da cewa ana daukar irin wannan tashin hankali a matsayin laifin yaki, kisan kare dangi ko manyan laifuka ga bil'adama. Ana gurfanar da masu aikata irin wadannan laifuka a gaban kotunan da suka cancanta;

4 Kasashe za su dauki matakan da suka wajaba don tabbatar cewa babu wani yaro, musamman ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18, da ke shiga tashin hankali, kaman musali daukan yara da ke cikin aikin soja.

Kudiri na 12: Incin bada ilimi da horo

14. Kasashe za su dauki dukannin matakan da suka dace domin:

15. kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata da kuma tabbatar da daidaito da samun ilimi da horo;

16. kawar da duk wani ra'ayi da ke haifar da irin wannan wariyar a cikin litattafai na makarantu, ko tsarin karatun boko da kuma kafofin watsa labarai;

17. kare mata, musamman 'yan mata, daga duk wani nau'i na cin zarafi, ciki har da cin zarafi a makarantu da sauran cibiyoyi koyarwa, tare da zartar da hukunci ga masu aikata wadannan laifuka;

18. a sa matan da aka zalunta ko cin zarafi da tsangwama su ci gajiyar samun shawarwari da basu kwarin gwiwa;

19. Saka tsarin daidaito na jinsi da bayar da ilimin kan yancin ɗan adam na yau da kullun a kowane mataki na tsarin bayar da ilimi a makarantu har ma wajen horas da Maluman makaranta.

2. Kasashe za su ɗauki mahimman matakai da nufin:

a. inganta ilimin mata;

b. inganta ilimi da horas da mata a kowane mataki da kowane fanni musamman a fannin kimiyya da fasaha;

c. inganta rajista da riko na diya mata a cikin makarantu da sauran cibiyoyin horaswa da tsara shirye-shirye ga 'yan matan da suka bar makaranta ba tare da sun kai lokacin barinta ba.

Kudiri na 13: Inci na tattalin arziki da kariya ta zamantakewa

Kasashe za su yi aiki da aiwatar da dokoki da sauran matakai da nufin tabbatar da daidaito ga mata wajen samun ayyukan yi, da ci gaba cikin ayyukan da suke yi, da samun damar yin kasuwanci.

Ta sabili da haka sun dauki alkawarin yin:

a) Inganta daidaito a fannin samun ayyukan yi

b) inganta incin samun daidaito na albashi ga maza da mata kan ayyukan yi masu daraja;

c) tabbatar da gaskiya wajen daukar ma'aikata, ko kara musu girma ko korar mata daga bakin aiki, zyaki da murkushe cin zarafin mata a wuraren aiki;

d) tabbatar wa mata yancin zabar aikinsu da kuma kare su daga cin zarafi da ci da gumunsu ko cin zarafi daga shugabanninsu na aiki, da muhimman hakkokinsu, kamar yadda yarjejeniyoyin, dokoki suka nunar;

e) samar da yanayi don ingantawa da tallafawa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin mata, musamman a bangaren kasuwanci na cikin gida;

f) samar da tsarin kariyar na inshora ta aiki ga matan da ke sana’o’insu na yau da kullum, sannan a wayar da kansu ta yadda za su amince da tsarin;

g) Kayyade mafi karancin shekarun na aiki, haramta ayyukan yaran da ba su kai wannan shekarun ba, sannan a haramta, da yaka ko murkushe duk wani nau'i na cin zarafin yara, musamman yara mata;

h) daukan matakan da suka dace don darajanta aiyyukan da mata ke yi cikin gidajensu;

i) tabbatar wa mata issashen lokacin hutun haihuwa da biyan su kafin haihuwar da bayan sun haihu a cikin kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati;

j) tabbatar da daidaito wajen biyan haraji tsakanin mata da maza;

k) A sanar wa mata masu albashi incinsu na cin gajiyar alawus-alawus daidai yadda aka bai wa mazan da ke da albashi domin biyan bukatun ma’aurata da iyallansu;

l) Amincewa da cewa babban nauyin ne ya rataya kan iyaye biyu miji ko mata wajen tarbi’antarwa da jin dadin rayuwar 'ya'yansu;

m) a dauki matakan da suka dace na doka da zartaswa don yakar cin zarafi da ake yi wa mata;

n) Kawo karshen tallace-tallace na batsa da ke a matsayin koma baya ga tsaron mutuncin su;

Kudiri na14: Incin samun kula da lafiya da kuma kula da lafiyar mata

Kasashe su tabbatar ana mutuntawa da habaka incin kula da lafiyar mata, da batun kiyaye lafiya wajen jima’i da haihuwa. Wadannan hakkoki sun hada da:

a) Incin aiwatar da binciken lafiya da kwayoyin haifuwa

b) Inci su ne su tsara yadda za su haihu da yawan ya’yan da za su haifa da kuma batun saka sarari tsakanin haihuwa ;

c) Samun inci na yin zabi da tsarin saka tazara tsakanin wannan da waccan haihuwar ;

d) 'yancin kare kai da kuma samun kariya daga cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i, har da cutar SIDA;

e) hakkin a sanar da su yanayin lafiyarsu da yanayin lafiyar abokan zamansu, musamman idan an kamu da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i, ciki har SIDA, daidai da tsarin ka'idoji lafiya na duniya;

f) Incin samun ilimi da karantaswa kan tsarin iyali

2. Kasashe su dauki dukannin matakan da suka dace saboba:

a) tabbatar da samun isassun ayyukan kiwon lafiya na mata, a farashi mai rahusa da kuma tazarar da ta dace zuwa gidajan asibiti, gami da basu bayanai, da wayar da kan mata, musamman mazauna karkara;

b) samar wa mata masu ciki kulawa ta musamman da bayan sun haihu da tsarin abinci mai gina jiki a lokacin daukar ciki da shayarwa da kuma inganta ma’aikatun da ake da su a wannan fanni;

c) kare hakkin haifuwa na mata, musamman bada izin nemarwa matan da aka yi musu ciki ta hanyar fyade ko cin zarafinsu ; sannan da bada izini ga likita don daukan mataki a lokacin da ciki ke barazana ga lafiyar kwakwalwa da ta jiki.

Kudiri na 15: Incin bada kariya a fannin samar da abinci

Kasashe za su tabbatar da 'yancin mata na samun lafiya da issashen abinci. Dangane da haka, suke daukar matakan da suka dace don:

a) tabbatar da samar da ruwan sha masu tsafta, da makamashi da ake amfani da shi a gida, da samun filaye da hanyoyin samar da abinci;

b) samar da tsarin samar da abinci da adano don tabbatar da wadatar abincin ga mata.

Kudiri na 16: Incin samun gidan kwana na gari

Mata suna da inci daya da maza wajen samun gidaje da yanayin rayuwa mai armashi a cikin yanayin da ba gurbatacce ba. Don haka, kasashe za su samar wa mata, duk kuwa matsayin da suke da shi na aure ko ba aure, don su sami matsuguni mai inganci.

Kudiri na 17: Incin kasancewa cikin yanayi na kyawawan al‘adu

Mata suna da inci rayuwa cikin yanayin da ke da kyawawan al‘adu, sannan incinsu ne su shiga a dama da su a kowane mataki na siyasar tafiyar da.

Kasashe su dauki dukannin matakan da suka dace domin samun mata cikin shinfida siyasar tsarin al’adu a kowane mataki.

Kudiri na 18: Incin kasancewa cikin yanayi kyaukyawa

Inci ne ga mata da su yi rayuwa cikin yanayin da ba gurbatacce ba kuma na kwarai.

1 Don haka kasashe za su dauki kwararan matakai don:

a) A tabbata an saka mata wajen tsarawa da gudanarwa da kuma kariya ta muhalli, da amfani da albarkatun kasa a dukannin mataki;

b) A karfafa neman masu zuba jari a fannin makamashi da ake sabuntawa da na sabin fusa’o‘i da suka dace, gami da sabin fusa’o’in bada labarai, da saukaka wa mata samun shiga cikin wannan tsari;

c) Karfafawa da bunkasa sanin da mata suke da shi a fannin fusa’o’i na gadin-gadin.

d) Kula da tsarawa gami da sarrafa tulin sharar da ake samarwa daga cikin gidaje ;

e) A kiyaye bin ka’idojin da suka dace na tarawa da sarrafawa da kuma fitar da shara da ka iya cutarwa.

Kudiri 19: Inci na samun ci gaba mai dorewa

Mata suna da incin su mori tsarin ci gaba mai dorewa. Ta haka ne kasashe ya kamata su dauki dukannin matakan da suka dace domin:

a) A rinka tunawa da saka tsari na daidaiton jinsi a duk tsare-tsaren da ake na ci gaban kasa

b) Ya kasance mata na cikin dukannin matakai na tsare-tsare da yanke shawara da aiwatarwa gami da mizani na siyasar ci gaban kasa ;

c) inganta samun dama ga mata da sarrafa albarkatu masu amfani, kamar filaye, da tabbatar da hakkinsu na mallakar dukiya;

d) Inganta yadda mata suke samun rance, horaswa, da samun kwarewa da kuma wallafawa a cikin karkara da birane domin samar musu da ingantacciyar rayuwa da rage musu talauci;

e) yin la'akari da alamun ci gaban Dan Adam musamman ga mata wajen fayyace manufofin ci gaba da shirye-shirye;

Kudiri na 20: Incin matar da mijinta ya rasu

Ya zamana kasashe suna daukan matakai da suka dace domin tabbatar cewa duk wadda mijinta ya rasu tana cin moriyar duk inci da Dan Adam ya kamata ya samu ta hanyar matakai kaman haka:

a) Kal matar da mijinta ya rasu ta fuskanci wulakanci da muzgunawa

b) Bayan rasuwar mijinta, mata ya kamata ta kula da yaranta, sai dai kuma idan yin hakan ba zai zame abun kwarai ga yaran ba ;

c) Wadda mijinta ya rasu tana da incin auren wani miji wanda take so ba tare da wani tilashi ba.

Kudiri na 21: Inci na samun gado

-Matar da mijinta ya rasu tana da incin samun wani kaso na arzikin da mijinta ya mallaka.

-Wadda mijinta ya rasu tana da inci zama a gidan da mijinta ya mutu ya bari. Idan ta yi aure tana da incin ci gaba da zama a gidan idan gidan nata ne ko kuma ta same shi ta hanyar gado.

1) Kaman maza suma mata suna da incin samun gado na iyayensu da suka rasu daidai da yadda doka ta tanada.

Kudiri na 22: Bada kariya ta musamman ga mata tsofaffi

Kan haka kasashe sun dauki nauyin cewa:

-za su bada kariya ga mata tsofaffi, tare da daukan matakai na musamman don kariyar jikinsu, da tattalin arzikinsu da dadin rayuwarsu har ma da batun samun aiki da ma horo idan har suna iya wa.

-Tabbatar da kariya ga tsofaffin mata daga muzgunawa, gami da cin zarafinsu ta hanyar fyade ko nuna musu wariya dangane da yawan shekarun da suke da su da kuma basu girmansu.

Kudiri na 23: Bada kariya ga mata nakasassu

Kasashe sun dauki nauyi kamar haka :

a) tabbatar da kariya ga mata nakasassu, musamman ta hanyar daukar matakai na musamman dangane da bukatunsu na zahiri, tattalin arziki da zamantakewa domin saukaka musu samun aikin yi, koyan sana’o’in hannu da kuma shigar da su cikin abun da ya shafi daukan mataki na kasa;

b) Tabbatar da kare nakasassu daga muzgunawa, gami da cin zarafi da nuna wariya ta sabili da nakasu da suke fama da shi tare da tabbatar da incinsu na kare mutuncinsu.

Kudiri na 24: Kariya ta musamman ga mata a cikin damuwa

Nan ma kasashe sun sha alwashi kaman haka:

a) tabbatar da kariya ga mata matalauta, shugabannin iyalai mata, ko mata daga kananan kabilu da kuma tabbatar musu da tsarin da ya dace da yanayinsu da kuma lura da bukatunsu na zahiri, tattalin arziki da zamantakewa;

b) tabbatar da kariya ga matan da ke da juna biyu ko masu shayarwa ta hanyar samar musu da tsarin da ya dace da yanayinsu da kuma incin kare musu mutunci.

Kudiri na 25: Saka mutane cikin incinsu

Kasashe sun sha alwashin :

a) bada garantin gyara da ya dace ga duk macen da aka take hakkita, kamar yadda wannan yarjejeniya ta tanada;

b) tabbatar da cewa a gaban hukumomin shari'a ne, ko wata hukuma ta gudanarwa da ke da izinin yin hakan aka karbi wannan haki.

Kudiri na 26: Aiwatarwa da bi sau da kafa

Kasashe za su tabbata aiwatar da wannan yarjejeniya a matakin kasa kuma su sanya a cikin rahotanninsu na lokaci-lokaci da aka gabatar daidai da kudiri na 62 na kundin Tarayyar Afirka, alamun dokoki ko wasu matakan da suka dauka don cikar hakkokin da aka amince da su a cikin wannan Yarjejeniya

1. Kasashe sun himmatu wajen aiwatar da duk matakan da suka dace da kuma ware isassun kudade cikin kasafin kuɗi da sauran albarkatu don aiwatar da dukannin hakkokin da aka amince da su cikin wannan yarjejeniya.

Kudiri na 27: Fasarawa

Kotun Afirka mai kula da kare hakkin bil'adama da al'umma, na da hurumin sauraron duk wata gardama da ta taso kan fassarar wannan yarjejeniya ko aiwatar da ita.

Kudiri na 28: Saka hannu, amincewa da kasancewa mamba

1 Ana gabatar da wannan Yarjejeniya ga kasashe da su sa hannu na amincewa da ita da kuma kasancewa mamba wanda za su yi aiki da yarjejeniyar daidai da tsarin mulkin su.

1. Matakan amincewa ko shiga cikin tsarin ana ajiye su ne a wajen shugaban shugaban hukumar Tarayyar Afirka.

Kudiri na 29: Soma aiki na yarjejeniyar

-Wannan yarjejeniya za ta fara aiki kwanaki talatin (30) bayan ajiye takardun shigarta -Zuwa ga kasashe mambobi da suka amince da wannan jarjejeniya. Matakin yarjejeniya na soma aiki ne daga ranar da aka ajiye takardun amincewa da ita.

-Shugaban hukumar Tarayyar Afirka, zai sanar wa kasashen da suka rattaba hannu lokacin soma aikin yarjejeniyar.

Kudiri na 30: Gyara da yin bita

1- Duk kasa mamba ka iya gabatar da shawarwari na gyara ko bitar wannan yarjejeniya.

2- Za a gabatar da shawarwarin gyara ko bita a rubuce, ga Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka wanda zai sanar da su da kasashe mambobi cikin kwanaki talatin (30) daga ranar da suka ajiye takardunsu.

3- Majalisar shugabannin kasashe da gwamnatoci, bisa shawarar hukumar Tarayyar Afrika, za ta binciki wadannan shawarwari a cikin shekara daya (1) bayan ta sanar wa kasashe mambobi, kamar yadda aka tanada a layi na biyu na wannan yarjejeniya.

4- Babban taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin kungiyar ne ke amincewa da shawarwarin da aka bayar na gyara ko bita da gagarumin rinjaye.

5- Kwaskwarima ko gyaran da aka yi, zai soma aiki ga kowace kasa da ta aminta da shi kwanaki talatin (30) bayan Shugaban Hukumar ta AU ya karba.

Kudiri na 31: Matsayin wannan yarjejeniya

Babu wani tanadi na wannan yarjejeniya da zai iya shafar tanadin da ya fi dacewa da hakkin mata, wanda ke kunshe a cikin dokokin kasa ko a cikin wasu yarjejeniyoyin yanki, nahiya ko na kasa da kasa, da suka shafi wadannan kasashen.

Kudiri na 32: Mataki na wucin gadi

Kafin a samu kafa kotun kare hakkin dan Adam da al’umma ta Afirka, hukumar kare hakkin dan Adam ta Afirka na da ikon sauraren hukuncehukuncen da suka shafi fassarar wannan yarjejeniya da ta samo asali daga aiwatar da ita.

Zama na 2 na babban Taron Kungiyar ne ya aminta da shi wanda aka yi a birnin Maputo a ran 11 ga watan Yuli na 2003.

About this version

RFLD translated the Maputo Protocol into Hausa in 2022 under the project “Tous pour le Protocole de Maputo” in Niger, with the support of the Swedish International Development Cooperation Agency (Sida). An audio version is also available.

The text was extracted from the PDF booklet and lightly formatted for the web. Some line breaks or headings may differ from the print version. The PDF remains available for download. Corrections: programs@rflgd.org.

Learn more: Maputo Barometer · free online course · all languages

SharefXinWA

For funders and partnersPour les bailleurs et les partenaires

Fund the women who defend rights in Africa, nowFinancez maintenant les femmes qui défendent les droits en Afrique

Aid to women’s organisations is falling. RFLD moves funding fast to women-led organisations and defenders, in French and English, through a network of 1,143 member organisations in more than 35 African countries.L’aide aux organisations de femmes recule. Le RFLD achemine vite les financements vers les organisations de femmes et les défenseures, en français et en anglais, grâce à un réseau de 1 143 organisations membres dans plus de 35 pays africains.

RFLD currently serves as Co-Chair of the SEA-T Programme Advisory Council, mandated to ensure the programme’s direction, priorities, and resources are meaningfully aligned with the visions of African women-led civil society. The SEA-T Programme is funded by the German Federal Ministry for Economic Cooperation and Development (BMZ) and implemented by the Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit (GIZ) GmbH.Le RFLD assure actuellement la coprésidence du Conseil consultatif du programme SEA-T, chargé de veiller à ce que l’orientation, les priorités et les ressources du programme soient réellement alignées sur les visions de la société civile africaine portée par les femmes. Le programme SEA-T est financé par le ministère fédéral allemand de la Coopération économique et du Développement (BMZ) et mis en œuvre par la Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit (GIZ) GmbH. See the partnershipVoir le partenariat

  • 1,143member organisationsorganisations membres
  • 35+African countriespays africains
  • N°553ACHPR observer statusstatut d’observateur CADHP
  • CandidPlatinum Seal of Transparency 2026Sceau de transparence Platine 2026

DonateFaire un don Partner with RFLDDevenir partenaire See our financialsVoir nos états financiers

Stay close to the movement.
Field notes, data releases and calls for proposals, in English or French. No more than one email a month.

Across all our workDans tout notre travail

Economic justice and climate justiceJustice économique et justice climatique

Women cannot be safe or equal without land, income and a voice in climate decisions. Economic and climate justice run through every RFLD programme, from ending violence to political leadership and health.Les femmes ne peuvent être en sécurité ni égales sans terre, revenus et voix dans les décisions climatiques. La justice économique et climatique traverse chaque programme du RFLD, de la fin des violences au leadership politique et à la santé.

Economic justiceJustice économiqueLand, work and the care economyLa terre, le travail et l’économie des soinsInheritance and land rights, decent work, credit for women and gender-responsive budgets.Droits successoraux et fonciers, travail décent, crédit pour les femmes et budgets sensibles au genre. Climate justiceJustice climatiqueWomen leading adaptationLes femmes à la tête de l’adaptationWomen-led adaptation, land rights, climate finance that reaches grassroots groups and a just transition.Adaptation menée par les femmes, droits fonciers, finance climatique qui atteint les groupes de base et transition juste. ProgrammeProgrammeRFLD Climate ActionRFLD Climate ActionOur programme for women’s leadership in the climate transition across sub-Saharan Africa.Notre programme pour le leadership des femmes dans la transition climatique en Afrique subsaharienne.
Stand with African women. Your support moves resources to the frontline.Partner with usDonate